News
Gwamnatin Kano Ta Kama ’Yan Kasuwa Kan Sauya Wa Madarar Gari Wa’adin Ƙarewa
Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano (KCPC) ta kama wasu ’yan kasuwa tare da rufe shaguna a Kasuwar Singer bisa zargin sauya wa madarar gari da wa’adin amfaninta ya ƙare sabon wa’adi domin sake sayar da ita.
Hukumar ta ce ta gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar shugabannin kasuwar, bayan samun bayanan sirri daga ƙungiyar ’yan kasuwar kan zargin aikata wannan laifi.
Rundunar Anti-Phone Snatching Ta Kama Mutane 10 Bisa Zargin Satar Wayoyi A Kano
A cewar hukumar, an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar al’umma da kuma hana yaɗuwar kayayyakin abinci da suka ƙare wa’adin amfani a kasuwanni.
Ta ƙara da cewa, sayar da kayan abinci da wa’adin amfaninsu ya ƙare na iya jefa lafiyar masu sayayya cikin haɗari, musamman idan aka yi ƙoƙarin ɓoye ainihin lokacin da ya kamata a daina amfani da su.
Sai dai hukumar ba ta bayyana sunayen ’yan kasuwar da aka kama ba, ko kuma adadin shagunan da aka rufe a yayin samamen.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News7 days ago
An Kwantar Da Dalibai 64 A Asibiti Bayan Shan Maganin Cutar Bilharzia A Katsina

