News
Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Kan Ciwo Sabon Bashin Dala Biliyan 7.7

Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon bashin kuɗaɗen waje har dala biliyan 7.7, kwatankwacin naira tiriliyan 10.79.
Tinubu ya gabatar da buƙatar ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya bayyana cewa ana buƙatar kuɗaɗen ne domin taimakawa wajen biyan gibin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai naira tiriliyan 20.2.
Shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gudanar da ayyuka da shirye-shirye a muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro, sufuri, noma, wutar lantarki, ilimi da lafiya.
Ya kuma bayyana cewa bashin zai taimaka wajen ƙara yawan ajiyar kuɗaɗen waje na Najeriya da kuma ƙarfafa darajar Naira.
-
News3 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News3 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News17 hours ago
Jami’an Ƴansanda 98 Ne Suka Mutu A cikin Watanni 10 A Sassan Najeriya — Rahoto
