News
Wani Matashi Ya Soka Wa Maƙwabcinsa Wuƙa Har Lahira A Kan Tsire

Wani matashi mai shekaru 21, mai suna Haggai Markus, ya rasa ransa bayan wani maƙwabcinsa mai shekaru 28, Ibrahim Augustine, ya soke shi da wuƙa a ƙirji a Jihar Adamawa.
Ana zargin lamarin ya faru ne sakamakon wata takaddama da ta ɓarke tsakanin mutanen biyu kan naman tsire a ƙauyen Mararaban Vimtim da ke Ƙaramar Hukumar Mubi ta Arewa a jihar.
Al’umma Ne Ke Da Ikon Zaɓen Shugabanni, Ba Jam’iyyun Siyasa Ba – Farfesa Fagge
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:00 na daren Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.
A cewar sanarwar, takaddamar ta samo asali ne daga gassasshen naman da aka ɗauka daga teburin wani mai tsire a yankin.
Ya ce yayin da saɓanin ke gudana, wanda ake zargin ya zare wuƙa ya soki mamacin a ƙirji.
Sanarwar ta bayyana cewa mahaifin mamacin, Markus Gabo, ne ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a daren ranar.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda daga ofishin Mubi ta Arewa sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da gawar mamacin cikin jini, tare da gano wata wuƙar girki da ake zargin ita ce aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.
Nguroje ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro, yayin da aka miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Ya ƙara da cewa za a ɗauki matakan gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
-
News4 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
