Connect with us

News

Dalibai Bakwai Sun Mutu Yayin Bikin Murnar Kammala Karatu A Jami’ar Nsukka

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Aƙalla dalibai bakwai na Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka, a Jihar Enugu, sun mutu yayin da suke gudanar da shagulgulan murnar kammala karatunsu a fannin hada magunguna.

Rahotanni sun bayyana cewa daliban sun halarci wani shagalin murna da suka shirya bayan kammala karatunsu, inda aka gudanar da bukukuwa da suka haɗa da kade-kade, raye-raye da shaye-shaye.

Jami’an Ƴansandan Kano Sun Kama Wani Barawo Da Ya Sace Wayoyi 222 A Kasuwar Farm Centre

Bayan kammala shagalin, an gano gawarwakin daliban bakwai, lamarin da ya jefa al’ummar jami’ar cikin alhini.

Sai dai har yanzu ba a bayyana a hukumance musabbabin mutuwarsu ba.

Mukaddashin Kakakin Jami’ar, Mista Inya Agha Egwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mahukuntan jami’ar tare da rundunar ‘yan sanda sun fara bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar daliban.

Advertisement

Ya kuma bukaci iyaye da ’yan uwan daliban da suka rasu da su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’ar hadin kai, yayin da ake ci gaba da bincike da tattara bayanai kan lamarin.

 

 

 TRIBUNE ONLINE 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending