Connect with us

News

An sako wasu ‘yan Najeriya 13 da aka kama a Poland

Published

on

Daga maryam bashir musa

 

 

 

 

Hukumomin ƙasar Poland sun sako ‘yan Najeriya 13 cikin 19 da suke tsare da su a sansanonin tsare ‘yan gudun hijira na ƙasar bayan yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine ya kore su daga Ukraine ɗin.

Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NidCom) ta ce an sako mutanen ne bayan saka hannun da jekadan Najeriya a Poland, Manjo Janar Christian Ugwu, ya yi.

Advertisement

An kama su ne bayan sun ƙi yarda su koma Najeriya lokacin da gwamnati ta ɗauki nauyin kwashe ‘yan ƙasar daga ƙasashe maƙwabtan Ukraine, kamar Poland da Romania da Hungary, a cewar NidCom.

A cewar jekadan, ɗaya daga cikin shidan da suka rage a hannun hukuma ya ce shi ɗan Kamaru ne saboda mahaifiyarsa ‘yar can ce.

“Abin baƙin ciki, sauran biyar ɗin sun nemi mafaka daga gwamnati…kuma ba za a sake su ba har sai gwamnatin Poland ta yanke shawara kan buƙatarsu ta amincewa ko kuma watsi da ita,” in ji Janar Ugwu.

Social embed from twitter

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending