News
KADA KOWA YA ZO DA WAYA AISHA TA SHIRYA LIYAFA GA YAN TAKARAR SHUGABAN KASA.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta gayyaci masu neman takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyu daban-daban zuwa Villa domin su yi buda baki tare.
Sai dai a wasikar gayyatan, an umurce su da tawo da katin gayyatarsu kawai sannan su ajiye wayoyinsu a gida
Za a yi taron ne da misalin karfe 6:30 da yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, a wani dakin taro na fadar shugaban kasa
Za a gudanar da taron shan ruwan ne a dakin taro na gidan gwamnati a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, da misalin karfe 06:30 na yamma.
Sai dai kuma, wannan umurnin bai shafi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni da ministocin da ake sanya ran zuwansu taron ba, Punch ta rwaito.
Nigerian Tribune ta rwaito cewa a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho, kakakin uwargidar shugaban kasar, Aliyu Abdullahi, wanda ya tabbatar da taron ya ce:
“Babu wani abu a nan. Wannan tsari ne na Villa idan kana da ganawa da daya daga cikin mazauna fadar shugaban kasa.
“Idan za su zo wani taro, wannan abu ne da ya kamata DSS su tilasta shi a lokacin da shugaban kasa ke wani taro ko mataimakin shugaban kasa na da wani taro ko uwargidar shugaban kasa na da wani taro. Saboda yan waje za su zo. Wannan shine tsaron da tsarin.
Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu
“Hakan bai shafi mataimakin shugaban kasa ba. Ta yaya za ka yi tsammanin hakan zai shafi mataimakin shugaban kasa koma ministoci?”
Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi 36 zuwa taron buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu.
Har ila yau, daga cikin wadanda shugaban kasar ya gayyata taron buda bakin harda manyan hafsoshin tsaro na kasar da wasu manyan jami’an gwamnati.
