Connect with us

Business

Tiwita ya tabbatar cewa ya kammala yin rajista a Najeriya

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Kamfanin sada zumunta na Tiwita ya sanar cewa ya yi rajista a matsayin kamfani karkashin dokokin Najeriya, cikin watanni bayan da kamfanin ya amince da sharuddan da gwamnatin kasar ta gindaya kafin ta kyale shi ya ci gaba da aiki a cikin kasar.

Advertisement

Najeriya ta dakatar da kamfanin a watan Yunin bara ne bayan da ya goge wani sako da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa.

Tiwita ya kare kansa, yana cewa sakon ya taka tsarin aikinsa, sai dai gwamnatin Najeriya ba ta gamsu da matakin ba.

Advertisement

Sai bayan wata bakwai Najeriya ta dage hanin wato a watan Janairun bana, shi ma sai da Tiwita ya amince da wsu sharudda, cki har da yin rajista a kasar kafin karshen watan Maris.

Wani wakilin kamfanin ya tabbatar wa BBC cewa kamfanin ya cika wadannan bukatun.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending