News
SAMA DA DALIBAI MILIYAN 18 BA SA ZUWA MAKARANTA A NIGERIA.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya bayyana damuwa bisa yadda kididdiga ke nuna cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ya kai miliyan 18 da rabi, kuma yana ci gaba da hauhawa.
Shugaban asusun a jihar Kano, Rahama Farah, wanda ya bayyana haka a wata tattaunawa da ‘yan jarida a kan shirin ilimin ‘yaya mata ya ce daga cikin yara miliyan 18 da dubu dari 5 din, miliyan 10 mata ne, wanda yake a matsayin kaso 60 na ilahirin adadin.
Ya bayyana damuwa a kan yadda kididdigar ta ta’azzara rashin daidaito a tsakanin jinsi, inda yarinya daya cikin ‘yaya mata 4 daga iyalan da basu da karfin tattalin arziki a yankunan karkara ne kawai suka kammala karamar sakandire.
Farah ya ce hare hare da ake kai wa makarantu da wasu cibiyoyin ilimi sun taimaka wajen rage rage dauki da yara ke yin a neman ilimi a fadin kasar, inda yace akwai yiwuwar hakan ya shafi karin ‘yaya mata fiye da maza.
Sai dai ya ce kawo dauki da asusun kula da kananan yara tare da gwamnati da sauran kungiyoyi suka yi, ya sa yanzu yara mata miliyan 1 da dubu dari 4 sun yi samu damar komawa makaranta.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
