Sports
Real Madrid ce mafi daraja a kwallon kafa a duniya
Daga kabiru basiru fulatan
Real Madrid ita ce ta daya a daraja a fannin tamaula a duniya kuma karo na hudu a jere in ji wani rahoto daga Brand Finance Football 50.
Kasuwancin da ake gudanar wa a kungiyar ya karu zuwa Yuro biliyan 1.5 tana gaban Manchester City Yuro biliyan 1.3 da itama Barcelona da take da Yuro biliyan 1.3.
Rahoton ya fayyace cewar kasuwancin Real Madrid ya karu a shekarar nan ta yadda ta bunkasa wasanninta da rawar da ta taka da hakan ya sa ta samu karin kudin shiga.
Rashan Cika Alkawari Yazama Dabi,ar Matasa Da Kuma Jagororin Al,umma-Kabiru Basiru Fulatan
A kan samu ci gaban kasuwancin kungiya ta hanyar cinikayyar ‘yan kwallo da samun manyan kamfanoni da ke daukar nauyin tallace-tallace da rawar da take takawa a gasar tamaula.
Jerin kungiyoyi 10 da ke kan gaba a daraja a fanni tamaula a duniya, gaban kungiyar Yuro biliyan da ta samu a 2022 ne:
- Real Madrid1.5
- Manchester City1.3
- Barcelona1.3
- Liverpool1.3
- Manchester United1.3
- Bayern Munich1.1
- PSG1.0
- Tottenham0.9
- Chelsea0.9
- Arsenal0.8
