Opinion
LOKACI YAYI DA MATASAN NAJERIYA YAKAMATA SU SAN KANSU-Alamin Yau Muhd
Daga Maryam bashir musa
Lokaci yayi da Matasan Najeriya yakamata su san kansu, duba da yanayin da kasar ke ciki na fatara da talauci da rashin aikin yi da matasan kasar ke ciki a wannnan lokacin
Alamin yace, a lokacin da tsananin rashin aikin yi ke karuwa a kasar, ‘yan siyasar kasar ko a jikinsu, domin wasu ‘yan siyasar kokari suke su saka ‘ya’yansu a kan kujerar mulki
kuma duk mai hankali yasan wadannan ‘yan siyasar ba sona nunawa talaka kana suke yi ba
ya bayyana hakanne lokacin da yake ganawa da wasu ‘yan jaridun kasar
inda yace lokaci yayi da Matasan Najeriya zasu san masu kaunar su ta hanyar sama musu abunyi, da maida wasun su makaranta domin su sami ilimi mai inganci.
yayi jan hankali akan matasan kasar domin gujewa duk wani abu da zai kawo rikici ko tashin hankali a zaben shekarar 2023.
ya kara dacewa matasa su guji shan miyagun kwayoyi ko daukar makami wajen gudanar da zabe a shekarar 2023.
yace matasa kar su bari zafin adawa yasa su cutar da kawu nan su, don haka matasa a guji bin ‘yan siyasar san kai da handama da baba kere, kirana ga Matasan Najeriya dasu jajirce wajen kawo sauyi a kasar nan,
