Connect with us

News

An tantance mai rajin kare shan wiwi a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a Kenya

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

An tantance wani dan siyasa da ke rajin kare shan tabar wiwi a Kenya, a matsayin dan takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a watan Agusta mai zuwa.

George Wajackoyah, wani lauya kuma Farfesa ya yi kokarin samun aikin ba tare da yin wani aiki sosai ba.

Amma a wannan karon, abin da ya sa a gaba a yakin neman zabe, na tabbatar da shan wiwi ya janyo masa goyon baya tun bayan kaddamar da takararsa a watan Fabirairu.

Ya kafa wata jam’iyyar siyasa da ake kira Roots da take son Kenya ta bari a rika sha da noman wiwi inda zai taimaka a biya bashin da ake bin kasar mai dinbin yawa.

A farkon wannan makon ne, aka yi watsi da yunkurinsa na takara saboda bai cika sharudan da ya kamata.

Advertisement

A ranar Alhamis kuma ya kara mayar da takardunsa inda aka tabbatar da takararsa saboda cika sharudan da aka shimfida.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending