News
AN KAMA YAN SARA SUKA DA BINDIGOGI A JAHAR NASARAWA
Daga Yasir sani Abdullahi
Rundunar Yan sandan jahar NASARAWA tayi nassarar kama Yan bangar siyasa su 24 a
Yansandan sunce sun kama wadanda ake zargin ne a minki da ke kan hanyar keffi zuwa akwangi na jahar
A wata takarda da ya rabawa manaima labarai Jami,in Hulda da Jama,a na rundunar yansandan jihar muyiwa adejobi yace Wanda aka kama yaran Wani Dan takarane na shekarar 2023
Ya Kara da cewa wadanda ake zargin sune suka ta-da zaune tsaye a jahar
Jami;an ‘yansandan sun kame wadanda ake zargin ne a wani otal bayan sun gama cin karensu ba babbaka.
Ya ce, daga cikin abubuwan da aka kama a hannun ‘yan sara-sukan akwai bindigogi guda takwasa da kuma wasu bindigogin na gargajiya guda biyu da kwanson harsasai guda talatin da bakwai da kuma riga guda hudu wadda harsashi ba ya iya huda ta.
Sauran abin da aka samu a hannunsu su ne watoti guda ashirin da bakwai sa wukake da kuma guru da layu. Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, su dai wadannan ‘yan sara-suka, wasu daga cikin ‘yansiyasa ke amfani da su wajen yin barazana ga abokan adawa, wani loaci har ta kan kai yin fada da zybar da jini
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
