Connect with us

News

ANA GAB DA FASALTA KUDIN TSARIN MULKIN LIBIYA

Published

on

''Yan kasar Libya sun kagu a gudanar da zabe R

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

 

fara taron masu ruwa da tsaki don fasalta kundin tsarin mulkin kasar Libya da Masar ke jagoranta a birnin Cairo, a wani yunkuri na ganin an gudanar da zaben kasar da ta shafe shekaru ta na fama da rikici.

SOJOJIN FARANSA SUN CAFKE KWAMANDAN IS A SAHEL

Advertisement

Shiga tsakanin na Masar bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da aka faro a Lahadin da ta gabata, shi ne karo na 3 da ake gudanarwa a kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar da kuma gudanar da zabe.

 

Ana saran a shafe fiye da mako guda ana zaman tattaunawar wanda zai bayar da damar bibiyar kundin tsarin mulkin kasar da zai bayar da damar gudanar da zabe a kasar.

 

Taron ya kunshi mambobin majalisar Libya, da na babban kotun kasar da kuma bangarorin masu bayar da shawarwari baya ga kwararru daga bangarorin siyasa dukkaninsu bisa sanya idanun Majalisar Dinkin Duniya.

 

Advertisement

Babbar jami’Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan rikicin na Libya ya roki bangarorin da ke cikin tattaunawar su samar da gamsasshiyar matsaya da za ta kawo karshen rikicin siyasar kasar.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending