News
Tsadar Mai: Gidajen Yada Labarai Na Fuskantar Durkushewa – Ramalan
Daga kabiru basiru fulatan
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Gidajen yaɗa labarai masu zaman kansu na ƙasa (IBAN) Dr Ahmed Tijjani Ramalan yace gidajen Talabijin da Rediyo masu zaman kansu a kasar na fuskantar barazanar daukewa dalilin tsadar man dizel.
Gwamnatin Kano ta zabi kamfanin jirgin sama daya tilo, don jigilan alhazan jihar
Ya kara da cewar gidajen Talabijin da Rediyo suna cikin mawuyacin hali biyo bayan halin da suka tsinci kansu na tashin gwauron zabo na abubuwan da suke bukata tun daga kan mai har ya zuwa sauran abubuwan da suke bukata na kuɗade domin biyan tauraron dan Adam.
Ramalan ya yi kira da babbar murya ga shugaban kasa da gwamnatin tarayya da yin gaggawar kawo musu dauki domin shawo kan matsalar.
“Kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin halin da kasar ta tsinci kanta bangaren rashin tsaro da matsalar tattalin arziki lamarin dake mayar da hannun agogo baya”
Ramalan ya kuma bayyana wasu manyan kalubale da kafafen yaɗa labaran ke fuskanta a halin yanzu da suka haɗa..
1- Ƙarancin Dalar Amurka a Bankuna da yadda musayar dala ya ɗaga sosai har ya haura ₦470 a dala da yadda hakan ya shafi harkokin kafafen sadarwar
2- Matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta wanda ya shafi harkar kasuwancin kafafen yaɗa labaran lamarin da ya sanya mafi yawan masu harkar a Legas suka zaftare farashin kasafin kudi da abubuwan da suke saye daga gidajen Talabijin da Rediyo masu zaman kansu musanman na Arewacin Najeriya
3- Matsalar yawan daukewar wutar lantarki a sassan kasar da tsananin tsadar man dizel da fetur ya tursasa dole gidajen yaɗa labarai rage yawan lokutan gabatar da shirye shiryen su, inda a halin yanzu litar man dizel ya haura ₦850.
4- Rashin bada da talla da tagomashi daga gwamnatin tarayya da jihohi ga gidajen Talabijin da Rediyo masu zaman kansu ya taimaka gaya wajen gurgunta ayyukan su.
“Wadannan abubuwan da na lissafo sune manyan abubuwan da ke ci wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu tuwo a kwarya dake jefa su cikin matsala”
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar shigowa ciki domin shawo kan matsalar domin kaucewa durkushewar gidajen Talabijin da Rediyo masu zaman kansu a ƙasar”.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
