News
Yan Sanda 6 Sun Mutu A Wani Harin Kwanton Bauna Da Aka Kaiwa Maniyyata Aikin Hajjin Jihar Sokoto
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shida daga cikin ‘yan sandan tafi da gidanka da suka yi artabu da ‘yan bindiga a lokacin da suka kai hari kan ayarin motocin alhazai a Sokoto, sun mutu a fafatawar da aka yi da su.
Alhazan da jami’an tsaron suna kan hanyar su ta zuwa Sokoto ne daga karamar hukumar Isa da ke jihar domin tafiya zuwa birnin Makka na kasa mai tsarki Saudiyya, domin gudanar da aikin hajji, inda ‘yan fashin suka yi musu kwanton bauna a dajin Gundumi.
An tattaro cewa an dawo da dukkan mahajjatan fadar Sarkin Gobir Isa ba tare da sun jin rauni ba.
Wani mazaunin garin Isa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Daily trust cewa ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sanda shida tare da kai gawarwakinsu zuwa Sakkwato.
“’Yan bindigar sun yi wa ayarin motocin kwantan bauna, wadanda ‘yan sandan tafi da gidanka dauke da muggan makamai suka jagoranta.
“’Yan sandan da ke gaba sun kama ‘yan bindigar na wasu mintuna, kuma hakan ne ya sa alhazan suka tsere yayin da motocinsu suka koma da baya zuwa karamar hukumar Isa,” inji majiyar.
An kuma tattaro cewa lamarin ya tilastawa hukumar jin dadin alhazai ta jihar sauya jadawalin tashin jirgin yayin da tuni aka dauke maniyyatan zuwa Sokoto.
Muhammad Bello, mai taimaka wa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kan harkokin yada labarai, ya ce jami’an gwamnati ne suka tarbi mahajjatan a babban birnin jihar, kuma ana gudanar da aikinsu na ci gaba da tafiya kasa mai tsarki.
Da aka tuntubi mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce ba a yi masa bayanin rasuwar abokan aikinsu a Isa ba.
Ya yi alkawarin yin magana a lokacin da ya dace.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
