Connect with us

News

Zan hidimtawa Kwankwaso a jam’iyyun NNPP da LP bakin gwargado — Bukarti

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Fitaccen lauya, Barista Audu Bulama Bukarti, yasha alwashin bada gudummawarsa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, idan har jam’iyyar NNPP ta hade da jam’iyyar LP, kuma ya kasancewa Kwankwaso ne dan takarar shugaban kasa.

Bukarti ya bayyana haka ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana mai cewa: “Indai Allah Ya taimaki Najeriya, NNPP ta yi nasara wajen hadaka da Labour Party Kwankwaso ya za ma dan takarar NNPP da LP, zan goyi bayan wannan ticket din ta dukkan hanyoyin da zan iya bada gudummuwa. Za mu fito mu yi kamfe iya iyawarmu domin mu ceto kanmu da kasarmu.”

Advertisement

Kwankwaso dai a halin yanzu shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, wanda kuma a yanzu haka ke tattaunawa da dan takarar jam’iyyar LP, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, domin ayi maja tsakanin jam’iyyun kuma suyi takarar shugaban kasa da mataimaki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending