News
Baza musaida Mai kasa da naira 180 ba Inji IPMAN
Daga Yasir sani Abdullahi
Kungiyar masu dillancin man fetur a Najeriya ta ce ta fara sayar da duk lita daya ta mai tsakanin N170 zuwa N190 tana mai cewa abu ne mai wahala su iya ci gaba da sayar da shi kan naira 165.
Jaridar The Nation ta ambato Sakataren IPMAN reshen Legas Akeem Balogun na cewa ”lura da yadda kasuwar take a yanzu, babu yadda za a yi mu sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita”.
Ya kara da cewa ”duk wani mamba da wata hukuma ta hana yin haka ya yi gaggawar sanar da uwar kungiya.”
An shafe watanni ana wahalar mai a Najeriya, musamman a manyan biranen kasar da suka hada da Abuja da Lagos.
IPMAN reshen na jihar Legas, ta ce rufe gidajen man wasu mambobinta ya kara haifar da dogayen layuka musamman a Lagos da Akure da Ado-Ekiti da Abeokuta da Jos.
-
News5 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News2 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News17 hours ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
