News
ADAMU YA BAYYANA DAMUWARSA KARARA KAN YADDA AKE FUCEWA DAGA APC
Daga Yasir sani Abdullahi
Shugaban jam,iyyar APC na kasa Abdullahi adamu ya bayyana damuwar kan yadda ake Fucewa daga jam,iyyar Apc
Bbc Hausa ta rawaito Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar.
Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.
Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.
Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar Edo.
Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Mista Adamu ya ce akwai takaici irin yadda yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.
” Ban damu da abinda ke faruwa a wata jam’iyya ba, damuwa ta itace abinda ke faruwa a jam’iyyata.”
” Babu Shugaba nagari da ba zai damu ba idan ya rasa mamba ko da daya ne a jam’iyyarsa, ballantana ayi maganar mamba biyu, ko uku.”, in ji Adamu.
Sai dai Shugaban APCn yace suna kan tattauna hanyar da zasu dinke wannan baraka ta ficewa daga jam’iyyar, duk da ya ce ba wani sabon abu bane
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
