Connect with us

News

Hukumar INEC ta Kara Wa’adin Rijistar Katin Zabe

Published

on

Daga Yasir sani abdullahi

 

Advertisement

 

Hukumar Zabe mai zaman kanta, INEC, ta amince da tsawaita wa’adin rijistar katin zabe da ake yi wanda a baya tace za a gama shi a karshen watan Yunin 2022. Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan lamurran zabe, Honarabul Aishatu Jibril Dukku, ta bayyana hakan yayin jawabi ga sauran ‘yan majalisar kan kokarin kwamitin wurin tabbatar da hukuncin da suka yanke makon da ya gabata.

Advertisement

Kwamitin yayi taro da INEC a ranar Talata kuma sun amince da kara wa’adin rijistar katin zabe da sauran bukatun da muka mika musu duk sun amince,” ta sanar da mambobin majalisar a ranar Laraba.

A ranar Laraba da ta gabata ne majalisar wakilan ta yi kira ga INEC da su kara wa’adin rijistar katin zabe da kwanaki 60 bayan ranar 30 ga watan Yunin 2022, domin bai wa ‘yan Najeriya damar rijista.

Advertisement

Majalisar ta yi kira ga hukumar da ta kara ma’aikata da kuma injinan yin katin zaben a fadin kasar nan domin a cimma manufa,

Shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar, Honarabul Benjamin Kalu, ya ce da farko za a kammala rijistar katin zaben kamar yadda hukumar tace a ranar 30 ga watan Yunin 2022 kafin zuwan zaben 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending