Connect with us

News

Sha’aban Sharada ya garzaya kotu domin canja Gawuna

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisement

 

Dan majalisar wakilai ta kasa na yankin karamar hukumar Birni daga jihar Kano, kuma shugaban kwamitin tsaro na majalisa, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya garzaya babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano, yana kalubalantar dan takarar gwamnan Kano da jam’iyyar APC ta tsayar, mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Advertisement

Sha’aban Sharada ta bakin lauyansa, Barista J.O Asoluka SAN, yace tsayar da Gawuna yaci karo da sashi na 84 (1),(3),(8),(12) da kuma (13) cikin baka da dokar zaɓe wacce aka yiwa gyara, domin masu rike da mukaman siyasa sun kada kuri’a a zaɓen fidda gwani, wanda kuma sashi na 84(13) ya soke damar haka, kamar yadda jaridar Solacebace ta rawaito.

Gawuna dai shi ne wanda jam’iyyar APC ta tsayar domin yi mata takarar gwamnan Kano a zaben shekarar 2023 mai zuwa, wanda ya kayar da abokin karawarsa, Sha’aban Ibrahim Sharada.

Advertisement

Karin bayani nanan tafe…

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending