News
Naira biliyan 187 ba zata isa aikin kidaya ba a Najeriya- NPC
Daga Yasir sani abdullahi
Hukumar Kidiya ta Najeriya ta sanar da cewa biliyan 187 da aka ware a kasafin kudi don kirga al’umma da gidaje, da aka shirya yi a watan Afrilun 2023.
Da Ɗuminsa: Kotun Ƙoli Zata yanke hukunci kan sashe 84 (12) na Dokar Zaɓe a yau
Shugabar hukumar ta riko Ugoeze Mbagou ce ta sanar da hakan ranar Alhamis, a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
An sake tada batun sake kidaya a Najeriya a karon farko bayan shekaru 17 da aka yi irinsa a 2006, wanda hakan ya saba shawarar Majalisar Dinkin Duniya da ta shata tazarar shekara 10.
Jaridun cikin gida sun ambaro Mbagou na cewa gudanar da kidaya a babbar kasa kamar Najeriya na bukatar kudin da ya haura naira biliyan 187.
Akan haka ta bukaci a sake duba kasafin kudin don duba yiwuwar kara wani abu.
Sai dai kuma ta ce rabin kudin kidayar zai fito ne daga kungiyoyin da ke bada tallafi ta wannan haujin.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
