Connect with us

News

SAAUYA SHEKA: FUSATATTUN SANATOCIN AOC SUN GANA DA BUHARI A ASO ROCK

Published

on

Daga khadija Abdullahi Mahmud 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Fusatattun sanatocin APC har 22 da suka sha alwashin barin jam’iyya baki daya sun samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattawa ne ya jagoranci sanatocin zuwa gaban Buhar inda suka tattauna ranar Talata

Advertisement

Kamar yada shugaban kasan ya bayyana, sauya shekarsu babbar barazana ce ga jam’iyyar dake da rinjaye a majalisar dattawa

Shirin Fim Ya Fi Min Siyasa – Mai Kwashewa

Advertisement

Shugaban tawagar sanatocin shine Santa Orji Uzoe Kalu, ya ce ‘yan majaliar basu ji dadin abinda ya faru ba ko kadan, Channels TV ta ruwaito

 

Advertisement

A yayin jawabi a taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga sanatocin da hakura da tunanin barin jam’iyyar.

Sanatoci masu yawa na jam’iyyar APC sun sauya sheka a cikin kwanakin nan.

Advertisement

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace sauya shekar babba barazana ce ga APC wacce ke da rinjaye a majalisar dattawa.

Advertisement

 

Bayan taron, Kalu yace fusatattun sanatocin sun fasa sauya sheka ko barin jam’iyyar baki daya.

Advertisement

 

“A safiyar yau, na jagoranci fusatattun sanatocin jam’iyyar APC 22 zuwa gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR,” Kalu, bulaliyar majalisa ta tara yace a wata takarda.

Advertisement

“Mun samu ganawa cike da nasara da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma batun sauya sheka daga jam’iyyarmu duk ya lafa,” yace.

 

Advertisement

Yawancin idan ba duka wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin tsayawa takara domin cigaba da tabbata a madafun iko ko tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023.

 

Advertisement

A kalla sanatoci bakwai na jam’iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa ko dai PDP ko kuma wata jam’iyyar adawa kafin zabe mai karatowa na shekarar 2023.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending