News
2023: Gwamnonin PDP shida sun yi fatali da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, -Sun lashi takobin zagon kasa.
Daga yasir sani Abdullah
Rikicin da ya kara daukar wani sabon salo a watan da ya gabata bayan bayyana gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takarar Atiku, ya faro ne makonni kadan bayan zaben Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Haƙƙin gyaran Arewa yana hannun al’ummarta ba wai shugabanninta ba-kabiru basiru fulatan
Kamar yadda shafin jaridar The Sun ya ruwaito, majiyoyin sun bayyana cewa, rikicin da ya barke a yanzu ya fafata da gwamnonin jam’iyyar PDP shida, wadanda galibinsu ‘yan Kudu ne, kuma sunyi watsi da takarar Atiku.
Majiyar ta bayyana wasu daga cikin gwamnonin sun hadar da Nyesom Wike na jihar Ribas; Samuel Ortom na jihar Benue; Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu; Seyi Makinde na jihar Oyo, Ishaku Darius na Taraba da Okezie Ikpeazu na jihar Abia, a matsayin gwamnonin da ba sa son goyon bayan takarar Atiku.
Gwamna Ortom ya ce, a cikin makon nan, shi fa ba zai yi aiki ba don tabbatar da takarar shugaban kasa na Atiku.
A cewar majiyar PDP rikicin ya faro ne a lokacin da aka zabi Ayu shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Majiyar ta ce shugabannin jam’iyyar sun amince da cewa za a mayar da shugabancin jam’iyyar PDP zuwa Arewa, yayin da ‘yan Kudu kamar yadda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi za su fitar da dan takarar shugaban kasa.
Majiyar wadda ba ta so a bayyana sunan ta, ta ce duk da yunkurin da gwamnoni da sauran shugabannin jam’iyyar suka yi na ganin Ayu ya mutunta yarjejeniyar da ya gada, amma Hakan ya ci tura.
Majiyar ta kara da cewa, a lokacin da Wike ya fadi zaben fidda gwani a hannun Atiku, shugabannin jam’iyyar sun amince cewa zai fi kyau a zabe shi a matsayin abokin takarar Atiku.
Ya bayyana cewa gwamnonin da muka ambata sun gana da Atiku da wasu shugabanni inda suka zabi Wike a matsayin zabin jama’a, amma Ayu da Atiku sun yi biris da su, wadanda ake kyautata zaton wasu manyan Arewa ne sukai hakan
Ya ce gwamnonin shida sun yanke shawarar kada su taka rawar gani a lokacin yakin neman zaben Atiku. Ya ce ko da yake ba za su sauya sheka zuwa APC ba, akwai yiwuwar su yi wa PDP zagon kasa.
“Gwamnonin ba za su iya ba kuma ba za su sauya jam’iyyar ba. sun fahimci hakan a fili. Idan sun sauya sheka, ’yan takararsu ba za su iya cin zabe ba. Wasu daga cikinsu sun gama mulki a karo na biyu. Amma za su yi wa Atiku zagon kasa kamar yadda gwamnonin PDP suka yi wa Shugaba Goodluck Jonathan zagon kasa a 2015.
“Idan za a iya tunawa, da yawa daga cikin gwamnonin PDP, musamman na Arewa, sun yi aiki don bullowar Buhari. Ba su zabi PDP ba, amma sun yi mata zagon kasa. Abin da zai iya faruwa kenan a lamarin Atiku.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
