Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasumatasa biyubisa zargin satar ragon Sallar wani mutum Sadiq Abolore wanda kudinsa ya kai Naira 120,000.
Gwamnati Ta San Za A Kai Harin Kuje, Ta Ki Yin Komai —Tukur Mamu
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mista Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana kama wadanda ake zargin.
Oyeyemi ya ce “An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da Sadik Abolore ya kai hedikwatar ƴan sanda da ke Ogijo.
Ya ce yanzu haka za a ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
