Connect with us

News

GIDAN YARIN KUJE: GWAMNATI TA FITAR DA SUNAYEN MUTANEN DA SUKA TSERE

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke nan Abuja a ranar Talata.

Advertisement

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ce ta fitar da jerin sunaye na mutum 69 a ranar Juma’a, kwana uku bayan kai harin.

Kungiyar Dillalan Man Fetur Ta Arewacin Najeriya ta Yi Barazanar Soma Yajin Aiki

Advertisement

A sakon da ta aika wa manema labarai, hukumar ta wallafa har da hotunan mutanen, kuma ta ce za a iya samun cikakken jerin sunayen a shafinta na intanet www.corrections.gov.ng/eccapees.

Hotunan na mutum 69 ne hukumar gidan yarin ta fitar, wadanda ta ce na ‘yan kungiyar Boko Haram ne da wasu daurarru wadanda shari’ar su take da nasaba da ta’addanci, amma suka arce daga gidan kurkukun bayan ‘yan bindiga sun fasa gidan.

Advertisement

Hukumar ta ba da wasu lambobin waya da ta ce ‘yan Najeriyar za su iya tuntubar ta ta layukan wayar, don sanar da jami’an ta duk wani bayanin da zai taimaka wajen cafke su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending