Connect with us

KABIRU BASIRU FULATAN

‎ ‎An haife ni a garin Fulatan, wanda ke a cikin Karamar Hukumar Rogo, Jihar Kano. Na girma cikin al’umma mai son ilimi da ci gaba, wanda ya ba ni damar samun ingantaccen ilimi tun daga matakin farko har zuwa gaba. ‎ ‎Karatuna ya fara ne daga Makarantar Firamare a Fulatan, inda na kammala tare da nasarori masu kyau. Bayan haka, na ci gaba da karatun Sakandire a Unity Karaye, inda na sami damar halartar Shirin Musanya Dalibai (Exchange Program School) wanda ya kara min gogewa da fahimta mai zurfi a harkokin ilimi da mu'amala. ‎ ‎Bayan kammala sakandire, na shiga Kano State Polytechnic, inda na karanci Mass Communication kuma na samu National Diploma (ND) a wannan fanni. Domin fadada ilimina a fannin tsaro da fasahar sadarwa, na ci gaba da karatu a National Academic of Server Security, inda na samu kwarewa a harkar tsaron bayanai da kula da (server security). ‎ ‎A fannin aiki, na samu damar yin aiki da gidajen rediyo daban-daban, ciki har da Aminci Radio da Gidauniya Radio Kano, inda na yi aikace-aikace masu nasaba da sadarwa da watsa labarai. ‎ ‎A halin yanzu, ina ci gaba da kokari a fannin da na zaba, tare da burin inganta fasahar sadarwa, tsaro a harkar bayanai, da kuma taimakawa al’umma ta hanyar kafafen watsa labarai. ‎

Stories By KABIRU BASIRU FULATAN