Connect with us

News

‎Mutane A Kauyen Jagalari Sun Nakasta Wani Da Ake Zargi Barawon Dabbobi Ne

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano
Spread the love

‎Mutane a kauyen Jagalari da ke Karamar Hukumar Fune a Jihar Yobe, sun nakasta wani da ake zargi barawon dabbobi ne

‎Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare, lokacin da matasan biyu Manu Ja’oji mai shekara 20 da Kabo Shungel, dukkansu daga kauyen Tashan Fulani a Karamar Hukumar Tarmuwa, suka shiga Jagalari da nufin satar dabbobi.

ICPC Ta Gurfanar Da Na Hannun Daman El-rufai A Kotu Kan Zargin Sama Da Faɗi Da Naira Biliyan 311

‎Shedun gani da ido sun ce al’ummar garin sunyi arangama dasu, lamarin da ya sa Manu Ja’oji ya jikkata sosai, yayin da abokin nasa ya tsere.

‎Jami’an tsaro sun garzaya wurin, tare da kai wanda ya jikkata Asibitin Babangida, daga bisani aka mika shi Asibitin Kwararru na Damaturu domin ci gaba da jinya.

‎Yanzu haka ana ci gaba da bincike tare da neman wanda ya tsere.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *