News
Gobara Ta Lalata Adaidaita Sahu 17 Da Tankokin Mai Biyu A Kano
Aƙalla adaidaita sahu 17 da kuma tankokin dakon man fetur guda biyu ne suka kone ƙurmus sakamakon Gobara biyu da suka tashi a wasu gidajen mai daban-daban a Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, Saminu Abdullahi, ya ce gobara ta faru ne a daren Talata.
Mutane A Kauyen Jagalari Sun Nakasta Wani Da Ake Zargi Barawon Dabbobi Ne
A cewarsa, gobarar farko ta tashi da misalin ƙarfe 8:45 na dare a gidan mai na AA Ayagi da ke ƙauyen Kanye, a kan titin Gwarzo, cikin ƙaramar hukumar Kabo.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani jami’inta, Muhammad Wada Abdulsalam, wanda ya sanar da tashin wutar.
Abdullahi ya ce jami’an kashe gobara daga sashen Rijiyar Zaki sun garzaya wurin, inda suka tarar da wata motar dakon mai na ci da wuta a lokacin da ake sauke fetur daga cikinta.
Motar, wadda ke dauke da lambar rajista XPB 999 FA kuma mallakar kamfanin AA Ayagi, ta riga ta sauke man daga sashe biyu, yayin da ake sauke sauran sassa uku masu dauke da kusan lita 5,000 lokacin da wutar ta kama.
Ya ƙara da cewa motar ta kone gaba ɗaya kafin jami’an su samu nasarar shawo kan wutar.
Gobara Ta Biyu
Kakakin hukumar ya ce an samu wata gobara ta biyu a gidan mai na Al-Wahida Nigeria Limited da ke Rimin Kebe Karshen Kwalta, a ƙaramar hukumar Nassarawa.
Motar da abin ya shafa, mallakar kamfanin BA Bello, mai lambar rajista KHX 29 XA, na dauke da kimanin lita 45,000 na man fetur a lokacin da gobarar ta tashi.
Ya ce wutar ta lalata kan motar da wani ɓangare na jikinta, tare da kone adaidaita sahu masu kafa uku guda 17 da ke ajiye kusa da wurin.
Sai dai jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan wutar, inda suka hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan Gidan man, lamarin da ya taimaka wajen rage asara.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarorin ba, sai dai hukumar ta ce za ta gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin faruwar lamarin.
