News
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Sama Da ‘Yan ISWAP 10 A Yankin Timbuktu Triangle
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta hannun sashen sama na Operation Hadin Kai (OPHK), ta hallaka fiye da mayaƙan ƙungiyar ISWAP 10 a hare-haren sama da ta kai a wasu sassan jihohin Borno da Yobe, ciki har da yankin da ake kira Timbuktu Triangle.
A cewar majiyoyin soji, an kai hare-haren ne a ranar 13 ga watan Janairu, bayan samun sahihan bayanan sirri daga jiragen leƙen asiri marasa matuƙa (UAVs), waɗanda suka gano taruwar mayaƙan ISWAP a kan hanyoyin Ambia Tasha, Ambia Sheruri, Ambia Turo da Shangamaru a Jihar Yobe.
Mutane A Kauyen Jagalari Sun Nakasta Wani Da Ake Zargi Barawon Dabbobi Ne
Rahotanni sun nuna cewa bayan tabbatar da sahihancin bayanan, rundunar ta kaddamar da hare-haren sama a kan wuraren da aka gano ‘yan ta’addan, inda aka lalata babura da wasu muhimman kayayyakin sufuri da suke amfani da su wajen kai hare-hare da zirga-zirga.
Majiyoyin sun kara da cewa farmakin ya haifar da mummunar asara ga ƙungiyar ISWAP, tare da rage musu ƙarfin motsi da shirin kai farmaki a yankin.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta jaddada kudirinta na ci gaba da kai hare-hare kan duk wasu kungiyoyin ta’addanci domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma a Arewa maso Gabas da kasa baki daya.
