Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Ma’aikata 3 Kan Sakacin Mutuwar Matar Da Aka Manta Almakashi A Cikinta

Published

on

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai tsaye Gwamnatin Kano
Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da ma’aikata uku biyo bayan mutuwar wata mata mai suna Aisha Umar, a Asibitin Abubakar Imam Urology Center da ke Kano, bayan zargin sakaci yayin yi mata aiki inda aka manta Almakashi a cikinta.

‎Wannan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Talata 13 ga Janairu, 2026.

Dakarun Soji Sun Kama Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Safarar Bindigogi A Taraba

‎Mijin matar ya ce aƙalla marigayiyar an shafe watanni huɗu tana jin ciwo a ƙasan marar ta bayan yi mata aikin, da aka je asibitin Mallam Aminu Kano, aka yi mata gwaji ne aka tabbatar da cewa an bar mata Almakashi ne a cikinta.

‎“Ana shirye-shiryen yi mata aiki ne ta Allah ta kasance a kan ta, Muna kira ga gwamnatin jihar Kano da ta yi duk mai yiyuwa domin bi mana haƙƙin A’isha Umar, domin za mu bi hakkin ta, in ji shi.”

‎Sanarwar ta ce a binciken farko Shugaban Hukumar, Mansur Mudi Nagoda, ya bayar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda aka dakatar da ma’aikata uku da ake zargi da hannu a lamarin daga dukkan ayyukan jinya nan take.

‎Sanarwar ta ƙara da cewa an mika batun ga Kwamitin Ɗaʼar Aikin Lafiya na Jihar Kano domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace bisa doka da ƙa’idojin aikin asibiti.

‎Hukumar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar Aisha Umar tare da jaddada cewa ba za ta lamunci sakaci ko saba ƙa’idojin aiki ba a dukkan asibitocin jihar ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *