News
Dakarun Soji Sun Kama Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Safarar Bindigogi A Taraba
Sojojin dake aiki a karkashin rundunar 6 Brigade, sector 3 da kuma ‘Operation Whirl Stroke’ sun kama wasu maza biyu da ake zargi da safarar bindigogi a jihar Taraba.
Mataimakin jam’in hulda da jama’a na rundunar Umar Muhammad wanda ya sanar da haka ya ce dakarun sun kama wadannan mutane bayan sun tattaro bayanan sirri da hada kai da mutane mazauna yakin.
Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Aike Da Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Gidan Yari
Jami’an tsaron dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Peace Shield’ tare da hadin gwiwar jami’an rundunar DIA na daga cikin jami’an tsaron da suka kama mutanen ranar Lahadin da ya gabata.
Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’an tsaron sun fara kama Christopher Adamu wanda aka fi sani da sunan ‘Suffer’ mai shekara 48 a wani wurin shakatawa Sebos Joint dake Mayo Dasa a karamar hukumar Jalingo .
“Jami’an tsaron sun dade sun fakon Adamu tare da tattaro bayanan sirri akan sa inda a wannan rana ne suka samu nasarar kama shi.
Sojojin sun kwato katin mafarauta daya, ATM biyu, katin dan kasa daya, wayar hannu kirar Itel daya, zobba shida, haka daya da layuka.
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa Adamu na da alaka da safarar muggan makamai musamman bindigogi.
Bayan ya shiga hannun jami’an tsaron Adamu ya tabbatar cewa yana gudanar da aiyukkan sa ne tare da taimakon wani mutum “Chmn” dake zama a Shomo Gari a karamar hukumar Karim Lamido.
Bayan jami’an tsaron sun kamo Adamu sannan da tattaro bayanan sirri ne suka kama wani James Yangyang mai shekara 37 a kauyen Tautre dake bayan kauyen Anguwan Bera a karamar hukumar Kola.
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa Adamu ya siyar da bindiga kirar AK-47 wa wani Bazor John dake zama a kauyen Murabus a karamar hukumar Ardo Kola tun a watan Nuwanba wanda hakan ke nuna ana hada-hadar safarar makamai a yankin.
Muhammad ya ce wadannan mutane na tsare a hannun jami’an sojoji inda nan da dan wani lokaci kadan za su damka su hannun jami’an tsaron da suka kamata domin ci gaba da gudanar da bincike.
Kwamandan rundunar 6 Brigade da Sector 3 da rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ Kingsley Uwa ya yaba da kokarin da jami’an tsaron suka yi wajen kamo masu safarar muggan makamai.
Uwa ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da sun samu nasarar dakile rashin tsaro a jihar da kasan gaba daya.
