News
Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Aike Da Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Gidan Yari
Wata mata maii suna, Nnenna Anozie, matar John Anozie, wanda tsofaffin jami’an rundunar SARS suka sace a watan Yunin 2017, ta nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta tsare babban sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, a gidan yari saboda zargin rashin mutunta kotu.
Mrs Anozie, ta shigar da wannan roƙo ne a ranar 11 ga watan Disambar 2025 inda ta zargi Egbetokun da ƙin yin biyayya ga umarnin kotun a watan Satumbar 2025 na kawo mata waɗanda suke da hannu a sace mijinta.
Jami’an NAPTIP Sun Ceto Wasu Yara 58 Daga Cikin 300 Din Da Suka Bace A Benuwe
Mai shari’a ya yi wannan hukunci ne a ranar 24 ga watan Satumba, inda mai shari’ar Binta Nyako da ke babbar kotun tarayya a Abuja, ta ba da umarnin sakin bayanan binciken ‘yan sandan da suke da hannu wajen sace mijinta da biyan ta diyyar Naira miliyan 2.
Sai dai Mrs Anozie ta ce ‘yan sanda sun yi watsi da wannan umarni inda ta yi kira da kotun ta gaggauta tsare babban sufeton wanda da shi take ƙara.
PREMIUM TIMES, a wani rahoto da ta fitar ta nuna tarihin yadda ‘yan sanda suka daɗe suna ƙin bin umarnin kotu da kuma lamarin ɓacewar Anozie.
Jami’an da ake zargi sun haɗa da Anthony Obiozor Ikechukwu, mataimakin sufurtandan ‘yan sanda da da Uzochukwu Emeana, wanda sajan ne da John Eze da Oriole wanda aka fi sani da T Boy da Sunday Okpe, sufurtandan ‘yan sanda.
Mrs Anozie ta ce jami’an ‘yan sandan waɗanda jami’ai ne na tsohuwar rundunar SARS a Awkuzu da ke jihar Anambra sun je har Lekki a jihar Legas inda suka sace mai gidanta a watan Yunin 2017.
Tun bayan lokacin ba a sake ganin mijinta ba kuma ba a gurfanar da shi a gaban wata kotu ba duk da umarnin da kotu ta bayar.
Game da ƙoƙarin neman adalci:
A yayin zaman kotun, Mrs Anozie, ‘yan sanda sun shaida wa kotu cewa Mr Anozie ya mutu ne a lokacin da suke tsare da shi. Amma sun sake gaza bin umarnin kotu wacce ta nemi su ba da gawarsa ko su yi bayanin yadda ya kai ga mutuwa.
Mrs Anozie ta shigar da kokenta gaban hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasa, (NHRC) wacce ta rubuta wa mahukunta da kwamitin duba lamarin #EndSARS a Abuja, sai dai ba wani sauyi saboda ba wanda aka kama cikin jami’an tsaro da sunan aikata wancan laifi.
A ranar 24 ga watan Satumba, Mrs Nyako ta babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan dokar ‘yancin samun bayanai da Mrs Anozie ta shigar a kan rundunar ‘yan sanda.
Mai shari’ar ta nemi babban sufeton ‘yan sanda ya bayyana ‘yan sanda da ake zargi da kuma bayanai da biyanta diyyar Naira miliyan 2.
Kotiun ta ba su umarnin ɗaukar waɗancan matakan a cikin kwanaki 7 daga ranar da ta ba da umarni.
Sai dai an shafe kwanaki ba tare da bin umarnin kotun ba.
Game da ƙin bin umarnin ‘yan sanda:
Tun watan Oktoba, lauyan Mrs Anozie, Vincent Adodo, ya fara aiki kan rashin bin umarnin kotu da IGP ya yi, tare da neman ba da takardar da za ta tilasta wa wanda ake ƙara bin umarnin kotu cikin awa 48 ko fuskantar fushinta.
Bayan shafe a wannin ne ta sake cike wani fom ɗin mai lamba 49 wanda ke neman wanda ake ƙara ya yi bayani kan dalilin da zai hana kotu tsare shi a gidan yari.
Haka dai babban sufeton yaƙi bin umarnin fom ɗin 48 wanda lauyan Mrs Anoze ya cike.
A ƙarshe dai sun nemi lallai a tsare babban sufeton a gidan yarin Kuje a Abuja har lokacin da zai mutunta umarnin kotu.
Kotun dai ta ayyana ranar 9 ga watan Fabarairu domin ci gaba da sauraron
