News
Jami’an NAPTIP Sun Ceto Wasu Yara 58 Daga Cikin 300 Din Da Suka Bace A Benuwe
Hukumar Hana Safarar mutane na kasa NAPTIP a ranar Talata ta bayyana cewa jami’an ta sun ceto wasu yara 58 daga cikin 300 din da suka bace a jihar Benuwe
Shugaban shiyar Hukumar dake jihar Benuwe Gloria Bai ta sanar da haka a taron da ta yi da manema labarai a garin Makurdi.
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Duk Da Shirin Gwamnatin Katsina Na Sakin Waɗanda Ke Tsare
Gloria wace shugaban aiyukka na Hukumar Yusuf Abdul ya wakilce ta a taron ya ce Hukumar ta ceto wadannan Yara a lotukata daban-daban.
Ta ce tun bayan bacewar yaran Hukumar a watan Mayu 2025 ta fara gudanar da bincike.
Gloria ta ce an ceto yaran a kauyukan Yelewata, Ukpam da Daudu dake karamar hukumar Guma.
Ta ce yaran na daga shekaru 2 zuwa 8 sannan jami’an hukumar sun kama wani Archbong shugaban wadanda ke tsare da yaran tare da wasu mutane hudu da suke tare da yaran.
Hukumar na tsare da wadannan mutane domin ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran yaran.
“Tun dama can yara 300 masu shekaru 2 zuwa 8 ne suka bace inda muka iya gano 20 daga cikin su a karamar hukumar Guma dake jihar Benuwe, jihar Nasarawa da Babban Birnin Tarayya Abuja wanda har an mai da su gida wurin iyayen su.
Gloria ta ce jami’an Hukumar sun kara gano wasu yara shida a gidajen marayu uku a Abuja da suma an hada su da iyayen su.
