News
Buhari ya naɗa Doyin Salami mai ba shi shawara kan tattalin arziki
- Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Dr. Doyin Salami a matsayin Babban Mai Ba da Shawara kan Tattalin Arziki.
Kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya faɗa a yau Talata cewa ana sa ran Dr. Salami zai yi wa Shugaba Buhari jawabi game da lamuran tattalin arziki na cikin gida da kuma muhawarar da ake yi a kan su.
Kazalika, zai dinga bin sawun abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasa da kuma wajenta tare da samar da tsarin da ya fi dacewa sannan ya bai wa shugaban ƙasa shawara a kan su.
Kafin naɗa shi a muƙamin, Dr. Salami mai shekara 59, shi ne shugaban kwamatin tattalin arziki na shugaban ƙasa.
‘Yan adawa da masana tattalin arziki sun daɗe suna sukar Buhari kan ƙin naɗa cikakken mai ba shi shawara kan tattalin arziki.