News
An maka mawaƙin nan Kahutu Rarara a kotu
Daga Kabiru basiru fulatan
Wata kotu ta gayyaci mawaƙin nan Dauda Kahutu Rarara da wani mai suna Alhaji Sunusi Sani a kan wata manaƙisa da ake zarginsu da ita. Masu ƙarar tasu dai suna zarginsu ne a kan wasu gine-gine da ake jin za su yi babakere a kai a unguwar Hausawa a birnin Kano.
Majiyar TDR Hausa ta jiyo masu ƙarar da suka haɗa da Ibrahim Lawal Rogo da wasu mutum biyar a ta bakin lauyansu Sunusi Ma’aji sun nemi a bi muau haƙƙinsu.
Yanzu haka dai ƙarar tana gaban mai shari’a Nura Ado Ayagi domin bin bahasi.