Hedikwatar tsaron Najeriya ta ja kunnen ‘yan siyasa da sauran mutane game da sanya kayan sojoji da yin amfani da wasu abubuwan nasu.
Makuddashin daraktan yada labarai kwamandan sojin saman Wap Maigida ne ya fitar da wata sanarwa kan hakan a ranar Alhamis.
Kakakin ya yi koke kan yadda ake sanya hotunan gwamnonin sanye da kayan sojoji.
Maigida ya bayyana hakan da yin abubuwan da suka wuce iyaka ga damar da ake bai wa mutane.
Ya kara da cewa babu abin da ya shafi sojoji da siyasa kuma ba su son tsoma baki a duk wani lamari na siyasa.
An shawarci fararen hula da su guji sanya kayan sojoji yayin tarukan siyasa