News
Sheikh Ahmad Bamba, ‘Kala Haddasana, na Kano ya rasu
Daga Yasir sani Abdullah
Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana ya rasu a yau Juma’a.
Wata jikarsa ta tabbatar wa da indaranka labarin rasuwar.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.