News
Sheikh Ahmad Bamba, ‘Kala Haddasana, na Kano ya rasu
Daga kabiru basiru fulatan
Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda aka fi sani da Kala Haddasana rasuwa a yau Juma’a.
Wasu iyalansa ne suka tabbatar wa da indaranka labarin rasuwar.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya inda ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.
Wani daga cikin ƴaƴansa Abdul ya shaida wa BBC cewa ya kusan shekara 82, don an haife shi ne a shekarar 1940.
Kala Haddasana kamar yadda aka fi saninsa da shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne kuma a can aka haife shi.
“Ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir.
“Ya koyar a fannin Islamic Studies kuma ya jima yana koyarwar,” a cewar ɗan nasa.
Malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda ɗan ya shaida mana.