Connect with us

News

Kano: Abdullahi Abbas ya dawo daga ƙasar Burtaniya cikin sirri

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

A jiya Juma’a aka ga fuskar shugaban jam’iyyar APC ɓangaren Gwamnatin Kano, Abdullahi Abbas Sanusi bayan shafe kwanaki 16 a birnin Landan shi da iyalansa.

Jaridar Labarai24 ta rawaito cewa Abdullahi Abbas wanda ƴan jami’yyar ke kiransa da Ɗan Sarki ya tafi hutu ƙasar Burtaniya a ranar 22 ga watan Disambar shekarar Bara tare da iyalinsa.

A lokacin ziyarar Abdullahi Abbas ya haɗu da mawallafin jaridar nan ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar wanda ya ke gudun hijira a ƙasar ta Ingila.

Advertisement

Tun da farko an hango fuskar Abdullahi Abbas ne a lokacin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi bakuncin Babban Khalifan Ɗariƙar Tijjaniyya na Duniya Sheikh Ali Bel Arabi a ɗakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano.

Ziyarar ta Abdullahi Abbas ta zo ne a lokacin da wata kotun tarayya ƙarƙashin mai shari’a Hamza Muazu ta soke zaɓen shugabannin jam’iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, tare da tabbatar da shugabannin da aka zaba a ɓangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau su ne halastattun shugabannin APC na jihar.

Sai dai wani abin mamaki da masu sharhi akan siyasar Kanon ke tambaya shi ne me ya sa Abdullahi Abbas ɗin ya dawo Najeriya cikin sirri ba tare da magoya bayansa sun yayata sanarwar dawowar ta sa daga wannan hutu da ya ne?.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *