News
2023: A.A. Zaura shine ɗan takarar mu — Ƴan Kannywood
Daga Yasir sani Abdullah
Jaruman Masana’antar Fim ta Kannywood sun baiyana goyon bayan su ga Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda a ka fi sani da A. A. Zaura a cikin ƴan takarar da ke neman zaɓen gwamna a Jihar Kano a kakar zaɓe ta 2023.
Jagoran ƴan fim ɗin, T. Y. Shaba ne ya baiyana haka jim kaɗan bayan ƴan Masana’antar sun karrama Zaura a jiya Asabar.
Shaba ya ce Zaura shine ɗan takarar ƴan Kannywood a jam’iyar APC a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne duba da irin hidimar da Zaura ke yi wajen tallafawa talakawa a jihar da ma wajen ta.
Ya ƙara da cewa Zaura ya zamo zakaran gwajin dafi wajen taimakawa masu ƙaramin ƙarfi ko da ba ƴan jam’iyar APC ba a faɗin jihar.
Ya kuma ce duba da irin hidimomin da ya ke na taimakon masu ƙaramin ƙarfi da kuma irin nasarorin da ya samu a rayuwar sa, sun samu yaƙinin cewa idan ya hau kujerar gwamnan Kano zai yi sama da haka kuma zai tallafawa Kannywood.
A nashi jawabin, Zaura ya gode musu a bisa lambar girma da su ka bashi.
Ya kuma nuna cewa ya kamata al’umma su fahimci ƴan Kannywood cewa su na fadakar da al’umma ne ta hanyar fina-finan su.