News
Ni ne ɗan takarar shugaban ƙasa da aka fi yayi a Najeriya – Dele Momodu
Daga muhammad muhammad zahraddin
Ɗan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation Magazine, Dele Momodu, ya ce shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa da “matasa suka fi yayinsa” a Najeriya.
Momodu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis ta kafar talabijin ta Channels TV jim kaɗan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP mai adawa.
Da aka tambaye shi ko zai iya ja da gogaggu kuma manyan ‘yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Mista Momodu ya ba da amsa da cewa shi aka fi yayi a Najeriya.
“Ba na so na yi alfahari. Babu wanda ake yayi kamata – ni ne wanda aka fi yayi a Najeriya. Ba wai ina magane a cikin PDP ba,” in ji shi.
Tun farko Dele Momodu ya kai wa shugaban PDP na ƙasa, Ayorchia Ayu, ziyara a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya miƙa masa wasiƙar nuna sha’awar tsayawa takarar a hukumance.
Ɗan jaridar ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2011 ƙarƙashin jam’iyyar National Conscience Party (NCP).
Ana sa ran gudanar da babban zaɓen a Najeriya cikin watan Fabarairu da Maris na shekarar 2023, inda PDP za ta nemi ƙwace mulki daga hannun APC ta Shugaba Buhari.