Connect with us

News

Buhari ga ƴan Nijeriya: Ya kamata ku yi wa gwamnati na adalci a kan rashin tsaro

Published

on

Spread the love

Daga muhMuham Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi wa gwamnatin sa adalci a kan rashin tsaro.

A cewar Buhari, ya kamata ƴan Nijeriya su tuna yadda ƙasar nan ta ke fama da rashin tsaro kafin ya hau mulki a 2015 da kuma gagarumar nasarar da gwamnatin sa ta samu a kan rashin tsaro, inda ya ce an ga bambanci ƙarara da kafin ya hau mulki.

Buhari ya faɗi hakan ne a yayin da Shugaban Ɗariƙar Tijjaniyya na Duniya, Tidjani Ali Bin Arabi ya kai masa ziyara a fadar shugaban ƙasa a Abuja tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da Sheikh Ɗahiru Bauchi, Shugaban darikar na Nijeriya a jiya Juma’a.

Advertisement

Buhari ya baiyana ƙwarin gwiwa cewa gwamnatin sa za ta kawo karshen rashin tsaro a wasu sassa na Nijeriya.

Shugaba Buhari ya bada misali da irin nasarorin da a ka samu wajen yaƙi da rashin tsaro a Arewa-maso-gabas, da Kudu-maso-Kudu, inda ya ƙara da cewa Arewa-Maso-Yammacin ƙasar ne ke da matsala kuma itama za a yi maganin rashin tsaron a nan.

Buhari ya yi kira ga ƴan ƙasa da su ɗauki harkar tsaro da muhimmanci a kan kan su sannan su riƙa yabawa irin ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi wajen samar da zaman lafiya.

Advertisement

“Mun yi iya kokarin mu kuma za ku ci gaba da jajircewa da samar da kudure-kudure na kwai karshen ta’addanci a ƙasar nan.

“Mu na rokon Allah Ya amsa addu’o’in mu,” in ji Buhari.

Shugaban ya yabawa gwamna Ganduje bisa gayyato shugaban Tijjaniyya ɗin kuma a ka yi wa ƙasa addu’a.

Advertisement

A nashi jawabin, Gwamna Ganduje ya gabatar da Ahugaban Tijjaniyyar da sauran ƴan tawogar sa da su ka haɗa da Sarkin Kano, Aminu Ado da Sheikh Ɗahiru Usman .

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *