Connect with us

News

Sarkin Kano ya ƙaddamar da gangamin rigakafin korona

Published

on

Spread the love

Daga YASIR SANI ABDULLAH

 

 

Advertisement

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ƙaddamar da gangamin rigakafin cutar korona a Karamar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa UNICEF ce ta shirya gangamin rigakafin da haɗin gwiwar Masarautar Kano.

A jawabin sa, Sarkin ya yi kira ga al’umma da su fito a yi musu rigakafin korona da sauran cututtuka, inda ya tabbatar da cewar rigakafin ba ta da wata illa ga jiki.

Advertisement

Ya kuma yi kira da a haɗa hannu guda wajen yaƙi da cutukan da su ke damun al’umma.

Haka ka taron ya haɗa da rigakafin lafiyar haihuwa da ta yara da sauran shirye-shirye na lafiya a jihar.

Ya kuma nuna alhini kan yadda yara ke fama da cututtuka irin su polio, ƴar lisuwa da kuma matsalolin haihuwa ga mata.

Advertisement

Ya kuma yabawa UNICEF da gwamnatin Kano a bisa kokarin da suke na bunƙasa harkar lafiya a Kano.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *