Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo Komawar Mourinho Everton, Barcelona da Munich na rububin Christensen

Published

on

Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

Kocin Roma Jose Mourinho mai shekara 58, ya ce a yanzu ya mayar da hankali ne kan ƙungiyar da yake jagoranci, sannan ya nesanta kansa daga aikin Everton bayan fitowar sunansa a jerin kwaca-kwacan da ake sa ran za su maye gurbin Rafael Benitez. (Sky Sports)

Newcastle tana kuma tunanin dauko Adana Demirspor da ɗan Italiya Mario Balotelli, mai shekara 31, a cewar shugaban kulob din ɗan Turkiyya Murat Sancak. (Inside Futbol via Star)

Advertisement

Paris St-Germain na tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba, mai shekara 28, da ɗan wasan tsakiyar Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 25, don dakko su daga Manchester United da AC Milan. Kazalika ƙungiyar na yunkurin shawo kan ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23 don ya ci gaba da zama a kungiyar a yayin da Real Madrid ke zawarcinsa. (ESPN)

Juventus ta tattauna da ɗan wasan gaban Faransa da Manchester United Anthony Martial amma har yanzu kungiyar ta Serie A ba ta tuntubi kulob din Old Trafford kan daukar dan wasan mai shekara 26 ba. (Goal)

Arsenal ta samu kwarin gwiwa a fatanta na sayen dan wasan tsakiya na Brazil da Juventus Arthur Melo, mai shekara 25 , yayin da shi kuma kulob ɗin na Italiya ke tattaunawa don sayen ɗan wasan tsakiyar Lyon dan kasar Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Get French Football via Sun) Martial

Advertisement

Juventus kuma ta nemi ɗan wasan tsakiya na Switzerland da Borussia Monchengladbach Denis Zakaria, mai shekara 25, don maye gurbin Arthur. (90mint)

Sai dai Arsenal ta fuskanci ƙalubale a zawarcin dan wasan gaban Fiorentina Dusan Vlahovic, mai shekara 21, inda ɗan wasan na Serbia ya ce yana son komawa Juventus ne kawai. (Mail).

Har yanzu Tottenham na kokarin siyan dan wasan Sipaniya Adama Traore a watan Janairu duk da cewa kocin Wolves Bruno Lage ya matsa kaimi wajen ci gaba da rike dan wasan mai shekaru 25 har zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Fabrizio Romano).

Advertisement

Brentford na iya fuskantar hamayya daga Leicester da Newcastle a yunkurinsu na sayen dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 29. (Times – subscription)

Dan wasan gaba na Croatia Ivan Perisic ba zai bar Inter Milan a watan Janairu ba duk da ana alakanta shi da Chelsea.

Kwantiragin dan wasan mai shekaru 32 zai kare a watan Yuni amma kungiyar ta Seria tana kokarin tsawaita kwantiraginsa. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Inter tana sa ido kan yanayin Paulo Dybala mai shekaru 28 a Juventus yayin da kwantiragin dan wasan na Argentina zai kare a bazara. (Gazzetto dello Sport via Mail)

Barcelona da Bayern Munich ne ke kan gaba wajen neman dan wasan bayan Chelsea Andreas Christensen, mai shekara 25.

Ɗan wasan Denmark ya ki amincewa da tayin da kungiyoyin Ingila suka yi masa saboda girmama kungiyar. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Har ila yau, Barcelona na shirin zawarcin dan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 22, daga Real Sociedad, idan har ta kasa daukar dan wasan gaban Borussia Dortmund na Norway Erling Braut Haaland, 21. (90mints)

Christian Benteke, mai shekara 31, ba shi da niyyar barin Crystal Palace a watan Janairu, duk da Burnley na ganin dan wasan na Belgium zai iya maye gurbin Chris Wood. (Evening Standard).

Dan wasan bayan Arsenal Pablo Mari, mai shekara 28, ya kusa komawa Udinese a matsayin aro. (Evening Standard)

Advertisement

Har wayau Arsenal da Tottenham da Leeds na zawarcin dan wasan Middlesbrough dan kasar Ingila Djed Spence, mai shekara 21, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Nottingham Forest. (Sky Sports)

Dan wasan bayan Fenerbahce da Hungary Attila Szalai ya ja hankalin West Ham da Newcastle, yayin da ita ma AC Milan kuma ke zawarcin dan wasan mai shekara 23, wanda aka kiyasta kudinsa kan fan miliyan 16.7. (Sky Sports)

Wakilin dan wasan baya na Amurka Sergino Dest ya ce dan wasan mai shekaru 21 na farin cikin zamansa a Barcelona yayin da ake rade-radin alaƙanta shi da Chelsea da Bayern Munich. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *