Connect with us

News

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta ragewa ƴan adaidaita-sahu kuɗin sabunta rijista zuwa N5,000

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Hukumar kula Da Tituna da Sufuri ta Jihar Kano, KAROTA ta cimma matsaya tsakaninta da matuƙa babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu kan biyan kuɗin sabunta rijista na shekara-shekara.

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne dai dubban matuƙa adaidaita-sahun su ka tafi yajin aiki domin nuna rashin amincewarsu da N8,000 kuɗin sabunta rijistar da KAROTA ta ce su riƙa yi shekara-shekara.

Da ga bisani ne sai matuƙa baburan su ka zauna da gwamnatin da wasu masu ruwa da tsaki, in da a ka shawo kan lamarin.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jamaa na KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hanu a yau Laraba, hukumar ta ce an cimma matsaya za su riƙa biyan N5,000 kudin rijistar, maimakon N8,000 da a ka sanya da farko.

Advertisement

Sanarwar ta ce an yi zaman yarjejeniyar ne a SakateriyaroƘungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, reshen Jihar Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an shafe fiye da awanni 4 a na tattaunawa da ɓangarori biyun, in da Barista Abba Hikima Fagge ya wakilci ƴan adaidaita-sahu, shi kuma Shugaban KAROTA, l Baffa Babba Dan’agundi da kuma Gamayyar Halastattun ‘Yan Ƙungiyoyin Adaidaita-Sahu na Jihar Kano.

A zaman na yau, in ji sanarwar, an amince da ragewa ƴan adaidaita-sahun biyan kuɗin shaidar tuƙi sabo daga N18,000 zuwa N12,000, in da sabunta wa kuma ya zama da ga N8,000 zuwa N5,000.

Advertisement

Zaman ya amince da biyan harajin kulum-kullum na N100, har da ranar Lahadi, wanda a baya sai dai su biya kuɗin ranar Lahadi ɗin a ranar Litinin.

Haka kuma zaman ya amince cewa kowanne ɗanan adaidaita-sahu ya biya wannan kuɗi nan da ƙarshen watan Febrairu na wannan shekarar, in da a ka ce ƙin biyan kuɗin a wannan lokacin zai sai a biya kuɗin baya kamar yadda zaman ya amince.

Jaridar indarankarawaito cewa, an gudanar da zaman ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Jihar Kano, Barista Aminu Sani Gadanya.

Advertisement

Da ya ke jawabin a wajen tattaunawar, Dan’agundi ya yabawa Shugaban Rundunar tsaro ta farin kaya, wanda bisa ga gudummawar da ya bayar ne a ka samu wannan matsaya.

Sannan ya bayar da tabbacin cewa KAROTA da matuƙa adaidaita-sahu sun samu kyakkyawar fahimtar juna a lokacin da su ke gudanar da tuƙi a kan titi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *