Connect with us

News

Katin Zabe: Tinubu ya yi amai ya lashe

Published

on

FB IMG 16427570908386435
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi amai ya lashe dangane da maganar da ya yi cewa wa’adin amfani da katin zabe ya kare,l.

A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Tinubun ya fitar, ya ce, jagoran na su ya yi kuskuren ambaton kalmar karewa a Ingilishi wato ‘expire’ ne maimakon ya ce, ”kila akwai bukatar a sabunta katin.”

Sanarwar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da kalaman na Tinubu ne suka janyo har hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta yi masa martani inda ta sheda wa BBC cewa wa’adin amfani da katin zaɓe bai ƙare ba, za a ci gaba da amfani da shi wajen kaɗa ƙuri’a.

Advertisement

Wani kwamishina ne a hukumar zaben bayan da BBC ta tuntube shi kan maganar ya faɗi hakan, bayan da wani bidiyo ya yaɗu a shafukan intanet da ke nuna Tinubu yana cewa wa’adin katin zaɓen ya ƙare.

A cikin bidiyon an ga Bola Tinubu da takunkumi a fuskarsa kuma zagaye da mutane, ana jinshi yana cewa “wataƙila ba za su gaya muku a kan lokaci ba… amma dai wa’adin amfani da katunan zaɓe ya ƙare.”

Sai kuma Tinubu ya ci gaba da cewa: “kuna buƙatar yaɗa hakan a ƙananan hukumomi da mazaɓu komai wahalar yin hakan.”

Advertisement

A 2021 ma a lokacin bikin cikar Asiwajun shekara 69 da haihuwa a Kano, jagoran na APC ya ce kamata ya yi a dauki matasa miliyan 50 a hukumomin tsaro na Nijeriya domin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar, amma kuma daga baya ya ce kuskure ya yi yana nufin dubu 50 ne, bayan da kalaman nasa suka tayar da kura.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *