Connect with us

News

Zan bar Najeriya fiye da yadda na same ta – Buhari

Published

on

FB IMG 16422460817653375
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa tana da kudurin ganin ta bar mulkin kasar fiye da yadda ta karbi mulkinta.

Shugaban ya kuma bukaci ‘yan kasar da su yi wa gwamnatinsa adalci a kan irin abubuwan da ta cimma zuwa yanzu, musamman ma alkawuran da ta yi kafin zaben 2015.

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya kai ziyara fadar Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammadu Isa II, a Kafanchan, yayin da ya je jihar Kaduna ziyarar kwana biyu domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *