Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo Makomar Diaz da Bentancur da Tielemans da Ndombele da Orsic, Alli da Aubameyang

Published

on

Spread the love

 Daga muhammad muhammad zahraddin

An yi watsi da tayin Tottenham na £38m kan ɗan wasan Porto asakin Colombia Luis Diaz, mai shekara 25. (Guardian)

Aston Villa na dab da cimma yarjejeniyar saye ɗan wasan Juventus asalin Uruguay Rodrigo Bentancur, mai shekara 24. (Football Insider)

Advertisement

Newcastle ba za ta iya saye ɗan wasan Brazil Diego Carlos ba saboda Sevilla ta yanke hukunci ci gaba da rike ɗan wasan mai shekara 28. (Fabrizio Romano)

Sai dai ƙungiyar ta gabatar da tayin kusan £30m kan ɗan wasan Lyon da Brazil mai buga tsakiya, Bruno Guimaraes. (Daily Mail)

Ɗan wasan Paris St-Germain da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 31, na shirin tafiya Arsenal(Sky Sports – via Daily Mail)

Advertisement

Liverpool da Manchester City na zawarcin ɗan wasan Leicester da Belgium Youri Tielemans. (Fichajes – via Leicester Mercury)

Juventus ta cimma yarjejeniya saye Dusan Vlahovic daga Fiorentina, hakan ya kawo karshen burin Arsenal na kwada sa’arta kan dan wasan mai shekara 21 asalin Serbia. (Goal)

Everton ta shiga sahun zawarcin ɗan wasan Tottenham da FaransaTanguy Ndombele, ɗan shekara 25. (Sky Sports – via TEAMtalk)

Advertisement

Brighton ta sa ido kan dan wasan Tottenham mai buga tsakiya Dele Alli don ganin ko zata iya aronsa, sai dai tuni ake alakanta matashin da Burnley, Everton da Newcastle(Mail)

Southampton na nazari kan Alli. (Telegraph – via Daily Echo)

Burnley na gab da daidaitawa da Dinamo Zagreb kan dan wasanta dan asalin Croatia Mislav Orsic, mai shekara 29. ((Sky Sports)

Advertisement

Ɗan wasan Everton Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 24, da ɗan wasan Wolves mai buga tsakiya Ruben Neves, ɗan shekara 24, da Douglas Luiz na Aston Villa’smai shekara 23, su kasance wadanda kocin Arsenal Mikel Arteta ke hari. (Athletic – subscription required)

Brentford ta kara kudin da ta gabatar da tayi kan dan wasan Nottingham Forest mai buga tsakiya, Brennan Johnson, haka zalika ana alakanta matashin ɗan shekara 20 da Newcastle(Independent)

West Ham na duba yiwuwar miƙa tayinta kan ɗan kasar Croatia nan da ke taka leda a MarseilleDuje Caleta-Car, sai dai tayin da suke gabatarwa na £20m bai gamsar ba. (Talksport)

Advertisement

Newcastle za ta rasa damarta na mallakar ɗan wasan tsakiyar Atalanta Robin Gosens lura da cewa Juventus na gab da cimma yarjejeniyar saye shi. (Goal)

Mai tsaron ragar Arsenal Bernd Leno, ɗan shekara 29, na fafutikar ganin ya bar emirates, kuma tuni Newcastle ta nuna zawarcinta a kansa. (Football.london)

AC Milan ta kwadaitu da ɗan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang. Ɗan wasan mai shekara 32 ya yi watsi da tayin da ya samu daga kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya. (Football Italia)

Advertisement

Ɗan wasan Red Bull Salzburg da Amurka Brenden Aaronson, ya ki amincewa da batun komawa Leeds United. (Yorkshire Post)

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *