Tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓen 2023.
Ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, inda shi kuma ya karanta ta a zaman majalisar na yau Laraba.
Okorocha wanda ɗan jam’iyyar APC ne mai mulkin Najeriya, shi ne tsohon gwamnan Jihar Imo na baya-bayan nan da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Shi ne mutum na baya-bayan nan da ya bayyana aniyarsa ta yin takara a APC a zaɓen da za a gudanar tskanin watan Fabarairu zuwa Maris na 2023.
Sauran waɗanda ke fatan su gaji Shugaba Muhammadu Buhari a APC sun haɗa da jagoran jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Ebonyi David Umahi, da tsohon Gwmnan Abia Sanata Orji Kalu.