News
2023: ACF ta gargadi mambobinta kan zaɓen ƴan takara
Daga Yasir sani Abdullah
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, ACF, ta gargaɗi mambobinta kan zaɓen ƴan takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa na 2023.
Audu Ogbeh, shugaban ƙungiyar kuma tsohon ministan noma ne ya baiyana hakan a jiya Laraba a jawabinsa na buɗe taron majalisar zartarwa ta kasa a Kaduna.
Ya ce ACF ba jam’iyyar siyasa ba ce, don haka ba za ta iya cewa ta na da ɗan takara mai neman shugabancin kasar nan ba.
Ya kuma ce ACF na shirin ganawa da ƙungiyoyi a yankin Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Yamma da kuma Kudu-maso-kudu a wani bangare na kokarin inganta zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya gabanin babban zabe.
“Shirinmu na yin taro da Afenifere, Ohanaeze, majalisar wakilan jama’ar kudu-maso-kudu har yanzu yana kan hanya domin akwai bukatar a dakatar da kalaman batanci ga wani yanki ko kuma wani yanki,” in ji shi.
“Ya kamata mu daina amincewa da kowane dan takara a zaben shugaban kasa a 2023. Idan wani ya tambaye ku game da amincewa, gaya wa irin wannan mutumin cewa mu ba jam’iyyar siyasa ba ce.
“Ko a 2023, har yanzu ba mu san ko wanene dan takarar ba. Mu ba jam’iyyar siyasa ba ce. Ba ma shiga harkokin siyasa sai inda ya zama dole.
“Allah Ya taimake mu da ‘yan takara nagari. Allah Madaukakin Sarki ne kadai zai magance mana matsalarmu,” in ji Ogbe.